Iran:Wata Tawagar Kungiyar Taliban Ta Kasar Afganistan Ta Iso Iran Don Tattauna Batun Zaman Lafiya A Afganistan

2021-01-26 14:54:10
Iran:Wata Tawagar Kungiyar Taliban Ta Kasar Afganistan Ta Iso Iran Don Tattauna Batun Zaman Lafiya A Afganistan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’id Khadib-Zade ya bayyana cewa wata tawaga ta kungiyar Taliban ta kasar Afganistan ta isa birnin Tehran da nufin tattauna batun zaman lafiya a kasarta.

Khadib-Zade ya kara da cewa twagar karshin shugabancin Mulla Abdul Ghani Barodar ta isa kasar Iran ne a safiyar yau Talta.

An shirya taron tattaunawa don dawo da zaman lafiya a kasar Afgansitan ne tun da dadewa amma kungiyar Taliban ba ta aiko wakilai ba sai yanzu.

Ana saran tawagar ta Taliban zata gana da jami’an gwamnatin kasar Iran wadanda suka hada da ministan harkokin wajen kasar Muhammad Javad Zarid da kuma jakadan kasar Iran a Afganistan, inda bangarorin zasu tattauna batun dawo da zaman lafiya a kasar ta Afganistan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!