Lebanon:Mutane 30 Ne Suka Ji Rauni A Zanga-Zangar Mutanen Kasar

2021-01-26 14:50:14
Lebanon:Mutane 30 Ne Suka Ji Rauni A Zanga-Zangar Mutanen Kasar

Wasu kafafen yada labarai a kasar Lebanon sun bada labarin cewa jami’an tsaron kasar suna ta fafatawa da masu zanga-zangar kin okar zaman gida ko kulle wacce gwamnatin kasar ta kafa a cikin matsi na tattalin arziki.

Kamfanin dillancin dalibai ISNA ya bayyana cewa mutanen birnin Beirut, Tarabulus da Saida sun fito zanga zangar nuna rashin amincewarsu da dokar kulle saboda dakile cutar korona a duk fadin kasar duk tare da matsalin tattalin arzikin da mutanen kasar suke fama da shi.

Labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai mutane 30 ne suka ji rauni a fatafawar da suka yi da jami’an tsaro.

A ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin kasar Lebanon ta kafa dokar hana fita ko kulle daga rannan, har zuwa 8 ga watan Fabrairu mai kamawa don dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Gwamnatin kasar ta Lebanon dai tana fama da matsalar yaduwar cutar korona a kasar da kuma matsalar tattalin arziki wadanda faduwar darajar kudaden kasar da kuma fashewar da ta auku a tashar jiragen ruwan kasar a cikin watan Augustan shekarar da ta gabata suka jawo.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!