Yemen:Sanya Ansarallu Cikin Jerin Kungiyoyin Yan Ta’adda Na Amurka Abin Alfakharine Ga Yemenawa

2021-01-26 08:50:21
Yemen:Sanya Ansarallu Cikin Jerin Kungiyoyin Yan Ta’adda Na Amurka Abin Alfakharine Ga Yemenawa

Wani mamba a kwamitin koli na siyasar kasar Yemen ya bayyana cewa sanya kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya abin alfahari ne ga mutanen kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammad Ali Al-Huothi ya na fadar haka a jiya Litinin bayan wani gangarumin gangami na yin Allah wadai da matakin da Amurka ta dauka na sanya kungiyar a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Al-Huothi ya bayyana haka ne a taron yin Allah wadai da Amurka a birnin Hudaida na bakin Tekun malia a jiya Litinin. An gudanar da irin wannan gangamin a wurare da dama a kasar.

A ranar 11 ga watan Jenerun da muke ciki ne, wato kwanaki 9 kafin sabon shugaban kasar Amurka ya karbi shugabancin kasar, gwamnatin shugaba Donal Trump ta sanya kungiyar ta Alsarallah cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda a wajenta.

Gwamnatin Amurkan da ta shude dai ta na da hannun dumu-dumu a zubar da jinin mutanen kasar Yemen wanda sarakunan larabawa karkashin jagorancin Saudia suke yi a kasar ta Yemen.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!