Chelsea Ta Kori Mai Horar Da ‘Yan Wasanta, Frank Lampard Bayan Faduwar Kungiyar A Wasanni Da Dama

2021-01-26 08:37:35
Chelsea Ta Kori Mai Horar Da ‘Yan Wasanta, Frank Lampard Bayan Faduwar Kungiyar A Wasanni Da Dama

A dai-dai lokacinda ake gudanar da gasar Premier League ta Engila, kungiyar Chelsea ta kori mai bawa yan wasan kungiyar horo Frank Lampard bayan kama aiki da watanni 18 kacal, saboda faduwa kungiyar a cikin wasannin da ta yi a baya-bayan nan

An kulla yarjejeniya ta horar da ‘yan wasan kungiyar Chelsea, Lampard na tsawon shekaru 3 a cikin watan yulin shekara 2019. Kafin a sallame shi dai Lampard dai ya jagorancin kungiyar London Blue zuwa matsyin na 4 a wasannin cikin gida, da kuma na FA ta karshe a aikinsa na farko.

Amma tun watan disamban da ya gabatar kungiyar Chelsea take yin baya har sai da ya kai ga an lallasata har sau 5 a cikin wasannin 8 da ta yi. Wanda hakan ya maida kungiyar bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da maki 11. A halin yanzu dai kungiyar tana neman wanda zai maye gurbinsa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!