Iran Ta Yi Maraba Da Shawarar Kafa Kawancen Tattalin Arziki Tsakanin Kasashe 6 Na Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran
Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Iran tana maraba da shawarar kafa kawance
mai karfi na tattalin arziki tsakanin kasashe shida na yankin.
Muhammad Jawad Zarif ya bayyana
hakan ne yau a lokacin da yake hanawa da shugaban kasar Azerbeijan Iham Aliyev
a birnin Baku fadar mulkin kasar, a wata ziyarar aiki day a fara gudanarwa a
yau a kasar.
Zarif ya ci gaba da cewa, Iran ta yi
maraba da shawarar da shugaban kasar ta Azerbeijan Ilham Aliyev ya
gabatar, ta kafa wani kwance na gungun kasashe shida na yankin, domin gudanar
da ayyuka na tattalin arziki a tsakaninsu, wato kasashen Azerbeijan, Turkiya,
Iran, Armenia, Rasha da kuma Georgia.
Ministan harkokin wajen kasar ta
Iran ya ce yin hakan zai kara karfafa ayyuka a bangaren harkokin kasuwanci da
tattalin arziki da cinikayya a tsakanin wadannan kasashe, kuma hakan zai
amfanar da dukkanin kasashen yankin ne baki daya.
Shi ma a nasa bangaren shugaban
kasar ta Azerbeijan Ilham Aliyev ya bayyana jin dadinsa da yadda Iran ta karbi
wannan shawara, kamar yadda kuma ya yaba da irin rawar da Iran ta taka wajen
ganin an kawo karshen rikicin da ya faru a watannin baya a tsakanin Azerbeijan
da kuma Armenia.
Ziyarar ta Zarif, bayan Azerbeijan
za ta hada da kasashen Turkiya, Armenia, Rasha da kuma Georgia.
015