​Pelosi Na Shirin Mika Wa Majalisar Dattijai Takardun Neman Gurfanar Da Trump A Kotu

2021-01-25 20:36:39
​Pelosi Na Shirin Mika Wa Majalisar Dattijai Takardun Neman Gurfanar Da Trump A Kotu

Shugabar majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi tana shirin mika takardun neman gurfanar da Trump a gaban kotu ga majalisar dattijai.

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, a yau ne ake sa ran Shugabar majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi, za ta mika takardun neman a gurfanar da Trump a gaban kotu ga majalisar dattijan kasar, bisa zarginsa da laifin tunzura magoya bayansa wajen kaddamar da farmaki a kan majalisar dokokin kasar.

Wannan lamari dai ya kawo rarrabuwar kai tsakanin manyan ‘ya’yan jam’iyyar Republican, jam’iyyar da Trump ya yi shugabanci a karkashin inuwarta, inda wasu daga cikin manyan ‘yan majalisar dattijai na jam’iyyar suke goyon bayan hakan, yayin da kuma wasu suke adawa da hakan.

Daga cikin sanatoci ya’yan jam’iyyar Republican masu goyon bayan hukunta Donald Trump, akwai masu ganin hakan shi ne daidai, domin kuwa ya sabawa doka kuma ya zubar da mutunci Amurka, da ma demukradiyya a kasar.

Masu adawa da batun gurfanar da shi daga cikin sanatocin jam’iyyar Republican kuwa, akwai masu ganin cewa yin hakan ba maslaha ce ga kasar ta Amurka ba, domin kuwa hakan zai iya jawo wasu matsalolin da ba a shirya yadadda za a tunkare su ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!