Najeriya Za Ta Kashe Dala Miliyan 100 Don Yakar Ta’addanci

2021-01-24 22:03:49
Najeriya Za Ta Kashe Dala Miliyan 100 Don Yakar Ta’addanci

Gwamnatin Najeriya ta alkawarta kashe dala miliyan 100 domin yaki da ta’addanci a kasar dama yankin.

Za’ayi amfani da dala miliyan 80 wajen murkushe kungiyar boko Haram a yankunan arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashin kasar.

Dala miliyan 20 kuwa Najeriya za ta baiwa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ne ta ECOWAS, domin yaki da ta’addanci, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ya shaidawa taron shugabannin kungiyar ECOWAS, na 58 da aka gudanar a jiya Asabar.

Tuni dai a cewar minsitan harkokin wajen Kasar, Geoffrey Onyeama, Najeriya ta bayar da umurnin fitar da kudaden zuwa ga asusun na Ecowas.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!