Zarif, Zai Ziyarci Kasashen Rasha, Turkiyya, Azerbaijan

2021-01-24 22:01:14
Zarif, Zai Ziyarci Kasashen Rasha, Turkiyya, Azerbaijan

A wani lokaci a gobe Litini ne ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, zai fara wata ziyarar aiki a kasahen Rasha, Turkiyya, Armenia, Azerbaijan da kuma Georgia.

Yayin ran gadin Mista Zarif, zai gana da takwarorinsa da wasu jami’an kasashen daban daban, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya Sayid KhatibZadeh, ya sanar.

Ziyarar dai za ta maida hankali kan alakar dake tsakanin Iran, da kasashen da batun samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!