Rasha Ta Bukaci Amurka Ta Daina Yi Ma Ta Shishigi

2021-01-24 21:57:20
Rasha Ta Bukaci Amurka Ta Daina Yi Ma Ta Shishigi

Kasar Rasha, ta bukaci Amurka data daina yi ma ta shishigi a harkokin cikin gida.

Wannan dai ya biyo ne bayan da ofishin jekadancin Amurka a birnin Moscow, ya ce yana goyan bayan ‘yancin ‘yan Rasha na yin zanga zangar lumana.

Kakakin fadar shugaban kasar Rasha, Dmitry Peskov ya bukaci Amurka data daina shishigi a harkokin cikin gidan kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!