Iran:Masu Bincike A Sun Gano Wata Hanyar Gano Cutar Korona Ta Nau’in Tarin Da Mutum Yake Yi

2021-01-24 14:14:26
Iran:Masu Bincike A Sun Gano Wata Hanyar Gano Cutar Korona Ta Nau’in Tarin Da Mutum Yake Yi

Wasu masana a jami’ar Shaheed Beheshti da kuma Jami’ar Sharif duk a nan birnin Tehran sun gano wata hanyar gano wanda ya kamu da cutar Korona ta hanyar amsafi da karar tarin wanda ya kamu da ita.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya bayyana cewa matasa masu binciken sun bayyana cewa wannan hanyar tana da inganci sosai wajen gano wadanda suke dauke da cutar.

Banda haka mutun yana bukatar daukar sautin tarinsa kawai cikin kasa da minti guda zai gano ko yana dauke da cutar ta korona ko babu.

Ganin yadda kudaden da ake kashewa wajen gwajin cutar ta Korona, wannan hanyar zata zama mai sauki sosai wajen gano wadanda suke dauke da cutar, amma da sharadin ya kaiga suna tari. Banda wasu alamomin cutar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!