Iraki:Akalla Mayakan Hashadushabi 11 Ne Kungiyar Daesh Ta Kashe A Arewacin Bangadaza

2021-01-24 13:52:55
Iraki:Akalla Mayakan Hashadushabi 11 Ne Kungiyar Daesh Ta Kashe A Arewacin Bangadaza

Wata majiyar jami’am tsaro a kasar Iraki ta bayyana cewa mayakan dakarun Hashadu Alsshabi 11 mayakan Daesh suka kashe a wani harin da suka kaimasu a arewacin birnin Bagdaza a jiya Asabar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tenhran majiyar tana cewa, mayakan na Daesh sun kaiwa runduna ta 22 ta Hashadu Alshabi ne garin Tikrit babban birnin Lardin salahuddeen a jiya Asabar a cikin duhu.

Wannan harin yana zuwa ne kwanaki biyu kacal da hare-haren kunan bakin wake suka kashe mutane 32 a wata kasuwa a cikin birnin Bagdaza.

Wani daga cikin dakarun Hashdu mai suna Abu Ali al-Maliki ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP kan cewa

Babu wanda ya dauki nauyin harin na Tikrit amma gwamnatin kasar tana tuhumar mayakan Daesh ta kai harin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!