Amurka:Gwamnatin Amurka Zata Sake Nazarin Yarjejeniyar Da Gwamnatin Da Ta Shude Ta Kulla Da Taliban

2021-01-24 12:22:57
Amurka:Gwamnatin Amurka Zata Sake Nazarin Yarjejeniyar Da Gwamnatin Da Ta Shude Ta Kulla Da Taliban

Sabuwar gwamnatin Amurka za ta sake nazarin yarjejeniyar zaman lafiya wacce gwamnatin da ta shude ta kulla da kungiyar Taliban ta kasar Afagnistan.Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto Jake Sullivan mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro yana fadar haka, a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Afganistan a jiya Asabar.

Sullivan ya kara da cewa, abinda gwamnatin za ta shi ne tabbatar da cewa kungiyar Taliban ta na aiki da yarjejeniyar. A nashi bangaren mai bawa shugaban kasar Afganistan shawara kan harkokin tsaro Hamdullahi Mohib ya ce bukatarsu ita ce tabbatar da zaman lafiya a kasar Afganistan.

A cikin watan Fabrairun shekarar ta da ta gabata ne, Amurka ta kulla yarjejeniya da kungiyar Taliban ta kasar Afganistan, da sharadin Amurka zata fidda sojojinta gaba daya daga kasar a karshen shekara ta 2021.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!