​Tarayyar Afirka Na Tattaunawa Da Rasha Kan Sayen Allurar Rigakafin Corona Ta Sputnik-7

2021-01-23 19:00:10
​Tarayyar Afirka Na Tattaunawa Da Rasha Kan Sayen Allurar Rigakafin Corona Ta Sputnik-7

Kungiyar tarayyar Afirka na tattaunawa da gwamnatin kasar Rasha kan batun sayen allurar rigakafin cutar corona ta sputnik-7 da Rasha ta samar.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, ofishin jakadancin kasar Rasha a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya bayar da bayanin cewa, yanzu haka ana tattaunawa tsakanin wakilan Kungiyar tarayyar Afirka da kuma gwamnatin kasar Rasha kan batun sayen allurar rigakafin cutar corona ta sputnik-7 daga kasar ta Rasha.

Bayanin ya ce kungiyar tarayyar Afirka na da nufin fara yin amfani da rigakafin na Rasha a cikin kasashen nahiyar Afirka, da zaran an cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin kasar Rasha kan hakan.

Yanzu haka wasu daga cikin kasashen duniya sun fara yin amfani da rigakafin na Rasha, da hakan ya hada da wasu daga cikin kasashen latin Amurka da nahiyar turai gami da nahiyar Asia, kamar yadda kuma daga nahiyar Afirka, kasar Aljeriya ce kawai ta fara yin amfani da rigakafin na sputnik-7 na kasar Rasha.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!