​Faransa: Wasu Musulmi Sun Yi Watsi Da Sabuwar Dokar Macron Dangane Da Muslunci

2021-01-23 18:42:48
​Faransa:  Wasu Musulmi  Sun Yi Watsi Da Sabuwar Dokar Macron Dangane Da Muslunci

Wasu daga cikin manyan kungiyoyin musulmi a Faransa sun yi watsi da dokar Macron da ke nufin kayyaye harkokin musulmi a kasar.

Jaridar Telegraph ta bayar da rahoton cewa, wasu manyan kungiyoyin musulmi guda uku a kasar Faransa sun yi watsi da dokar Macron a kan musulmi wadda ke nufin raunana su da kuma take hakkokinsu a kasar.

Rahoton ya ce, babban kwamitin musulmin kasar Faransa (CFCM) da aka kafa tun shekaru 20 da suka gabata, ya sanya hannu kan dokar tare da matsin lamba daga gwamnatin Macron, inda bangarori takwas na musulmin kasar ne suka halarci zaman, amma bangarori uku sun ki sanya hannu, yayin da bangarori biyar suka sanya hannu.

Wadanda suka ki sanya hannu sun bayyana cewa, akwai tauye hakkokin musulmi a cikin wannan doka, domin kuwa dokar ba an kafa ta kan mahanga ta dimkradiyya ba ne, saboda haka amincewa da dukkanin abin da ta kunsa, na nufin musulmi sun amince da abin da ake jingina musu kenan bisa zalunci.

Tun bayan kisan wani malamin makaranta a shekarar da ta gabata a kasar Faransa wanda yake yin izgili da manzon Allah (SAW) Macron yay a fito fili ya bayyana goyon bayansa ga masu aikata hakan, tare da bayyana cewa ‘yancin fadar albarkacin baki da bayyana ra’ayi ne, lamarin da ya fusata musulmi a duniya baki daya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!