Sabuwar Gwamnatin Amurka Ta Ce Za Ta Yi Dubi Kan Sanya Ansarullah Cikin Kungiyoyin Ta’adanci Da Trump Ya Yi

2021-01-23 14:30:40
Sabuwar Gwamnatin Amurka Ta Ce Za Ta Yi Dubi Kan Sanya Ansarullah Cikin Kungiyoyin Ta’adanci Da Trump Ya Yi

Sabuwar gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta sanar da cewa za ta sake dubi cikin matsayar da tsohuwar gwamnatin Donald Trump ta ɗauka na sanya ƙungiyar Ansarullah ta ƙasar Yemen cikin ƙungiyoyin ta’addanci na duniya.

Mutumin da Shugaba Biden ɗin ya miƙa sunansa ga majalisar ƙasar a matsayin wanda yake so ya zama sakataren harkokin wajen Amurkan, Antony Blinken, ne ya sanar da hakan inda ya ce lalle nan ba da jimawa ba gwamnatin Biden ɗin za ta sake dubi kan wannan matsayar, saboda a cewarsa gwamnatin ba ta son duk wani abin da zai kawo cikas ga isar da kayayyakin agaji zuwa ga al’ummar ƙasar ta Yemen.

Tun dai bayan da aka rantsar da Joe Biden ɗin a matsayin sabon shugaban AMurka a ranar Larabar da ta gabata ne cibiyar kula da isar da kayan agaji ta kasa da kasa ta bukaci ta bukaci gwamnatin Amurka da ta soke wannan dokar ta sanya Ansarullah ɗin cikin ƙungiyoyin ta’addanci don gujewa bala’in da zai samu al’ummar Yemen ɗin na rashin isar kayayyakin agaji gare su.

Har ila yau manyan jami’an MDD da kuma kungiyar agaji ta Red Crescent ta duniya sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da irin mummunan tasirin da sanya Ansarullah ɗin cikin kungiyoyin ta’addanci da gwamnatin Trump ɗin ta yi ga al’ummar ƙasar Yemen.

A kwanakin baya ne dai tsohon sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo ya sanar da sanya Ansarullah ɗin cikin ƙungiyoyin ta’addanci a mahangar gwamnatin Amurkan, lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine daga ɓangarori daban-daban na duniya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!