Firayi Ministan Iraƙi Yayi Kwaskwarima Ga Cibiyoyin Tsaron Kasar Bayan Harin Ta’addancin Bagadaza

2021-01-23 14:21:04
Firayi Ministan  Iraƙi Yayi  Kwaskwarima Ga Cibiyoyin Tsaron  Kasar  Bayan Harin Ta’addancin  Bagadaza

Firayi ministan ƙasar Iraƙi, Mustafa Al-Kadhimi ya sallami wasu manyan jami’an tsaron ƙasar daga muƙaminsu a matsayin wani ɓangare na kwaskwarimar da yake yi wa tsarin tsaro na babban birnin ƙasar, Bagadaza, bayan mummunan harin ta’addancin da a ka kai birnin a ranar Alhamis din da ta gabata, yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa barin sake abkuwar hakan ba.

Firayi ministan na Iraƙi ya ɗau wannan matsaya ce bayan ya jagoranci wani taro na majalisar tsaron ƙasar Iraƙin a jiya Juma’a don tattauna matsalar tsaron da aka fuskanta da ta yi sanadiyyar kai wannan harin da ake ganinsa a matsayin mafi girma da munin harin da aka kai ƙasar tun a shekara ta 2018.

A yayin zaman dai firayi minista al-Kadhimi, wanda kuma shi ne kwamandan sojojin Iraƙin ya bayyana cewar lalle akwai matsala cikin tsarin tsaron birnin na Bagadaza, wanda wajibi ne a yi maganin hakan cikin gaggawa.

Sai dai kuma a ɓangare guda firayi ministan na Iraƙi ya yaba wa ƙoƙarin da cibiyoyin tsaron Iraƙin suke yi tsawon watannin da suka gabata na nasarorin da suka samu wajen daƙile ƙoƙarin ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh wajen shigowa birnin na Bagadaza da kai hare-haren ta’addanci.

Harin na ranar Alhamis dai da aka kai wata kasuwa a birnin na Bagadaza yayi sanadiyyar mutuwar alal aƙalla mutane 32 da kuma raunana wasu sama da 110 bayan wasu ‘yan ƙunar baƙin wake su biyu suka tarwatsa kansu a cikin jama’a. Kungiyar ta’addancin nan ta Daesh (ISIS) dai ta ɗau alhakin kai wannan hari.

Ƙungiyoyi daban-daban na Iraƙin dai sun zargi ƙasashen Saudiyya da UAE da hannu cikin wannan hari ta hanyar irin goyon bayan da suke ba wa ‘yan ta’addan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!