​Iraki:An Kai Hari Na 6 Kan Tawagar Sojojin Amurka A Cikin Kwanaki Biyu A Jere

2021-01-23 10:01:41
​Iraki:An Kai Hari Na 6 Kan Tawagar Sojojin Amurka A Cikin Kwanaki Biyu A Jere

Majiyoyin labarai daga kasar Iraki sun nuna cewa an kai hari na 6 kan tawagar sojojin Amurka a kasar a cikin kwanaki biyu da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Sabirin na kasar ta Iraki ne ya bayyana haka a daren jiya jumma’an. Ya kara da cewa an kai hari kan tawagar sojojin Amurkan ne a yankin Salahuddin da ke tsakiyar kasar inda aka jawo mata asosri masu yawa.

Wannan dai shi ne hari na 6 kan tawagogin sojojin Amurka a kasar Iraki a cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Mutanen kasar Iraki dai suna bukatar ficewar sojojin Amurka daga kasarsu. Har ma majalisar dokokin kasar ta kafa dokar ficewar dukkan sojojin kasashen ketare daga kasar a farkon shekarar da ta gabata, bayan da Amurka ta yi wa Janar Shahid Kasim Sulaimani da abokin tafiyar sa kissan gilla.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!