IMN Ta Bukaci A Saki El-Zakzaky Da Matarsa Bayan Bullar Cutar Korona A Kurkukun Kaduna.

2021-01-23 09:31:35
IMN Ta Bukaci A Saki El-Zakzaky Da Matarsa Bayan Bullar Cutar Korona A Kurkukun Kaduna.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta musulunci wacce take da cibiya a birnin London na kasar Burtaniya wato ‘Islamin Human Right Commision (IHRC)’ ta bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Malama Zinat Ibrahim bayan da ta kamu da cutar korona a cikin gidan yari na birnin Kaduna inda ake tsare da su.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kungiyar har’ila yau ta rubutawa MDD kan wannan batun, don ta takurawa gwamnatin shugaba Buhari ta saki sheikhin malamin.

A wani labarin kuma kungiyar harka Islamiya ko IMN ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Nigeriya na ta bawa Malama Zinat matar Sheikh Elzakzaky damar zuwa asbiti don jinyar cutar korona wacce ta kamu da ita a cikin yan kwanakin da suka gabata.

A ranar litinin 25 ga watan da Muke ciki ne ake saran za’a saurari karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar kan Sheikh Elzakzaky da Matarsa, wadanda ake tsare da su tun shekara ta 2015 duk tare da cewa wata kotu ta bukaci a sake su.

A ranar Alhamis da ta gabata ce Muhammad Ibrahim Elzakzaky ya bada sanarwan cewa mahaifiyar Malama Zinat Ibrahim ta kamu da cutar korona a gidan yarin kaduna amma har zuwa lokacinda yake bada rahoton hukumomi sun ki kaita asbiti don jinyar cutar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!