Gwamnatin Sin Ta Bawa Sojojin Ruwa Na Kasar Damar Bude Wuta A Kan Jiragen Ruwan Kasashen Waje Idan Akwai Bukatar Hakan

2021-01-23 09:04:19
Gwamnatin Sin Ta Bawa Sojojin Ruwa Na Kasar Damar Bude Wuta A Kan Jiragen Ruwan Kasashen Waje Idan Akwai Bukatar Hakan

Majalisar koli ta jam’iyyar ‘The National Peaple Congrass” mai mulkin kasar ta amince da doka wacce ta bawa sojojin ruwan kasar damar bude wuta kan duk wani jirgin ruwa da ya shigo tekun kudancin kasar sin, idan sun ga ya zama barazana ga kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne a jiya jumma’a, ta kuma kara da cewa sojojin suna da damar amfani da duk hanyoyin da suke da sun don hana jiragen ruwan kasashen waje shiga ruwan kudancin kasar.

Kasar Sin dai ta na daukar dukkan ruwan da ke kudancin kasar a matsayin mallakinta. Daga cikin ruwan yakin kudancin Sin ne jiragen ruwa dauke da kayaki na kimani dalar Amurla tiriliyon 3.4 suke wucewa a ko wace shekara.

Kasashen Vietnam, Taiwan, Philippines, Malaysia, da Brunei duk suna ganin suna da rabo a tekun na kudancin Sin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!