Harin Isra’ila A Siriya Ya Yi Ajalin Mutum Hudu Ciki Harda Yara

2021-01-22 16:08:31
Harin Isra’ila A Siriya Ya Yi Ajalin Mutum Hudu Ciki Harda Yara

Siriya, ta sanar da sake murkushe wani harin makamai masu linzami na Isra’ila a yankin Hama, kamar yadda kamfanin dilancin labaren kasar ya rawaito.

Wata majiyar soji ta ce an kai hare haren ne wajajen karfe hudu na daren jiya, kuma makamman garkuwa na kasar sun kakkabo dayewa daga cikin makamman da Isra’ilar ta harba.

Saidai an samu hasarar rayukan mutum hudu wasu iyalai mata da miji da ‘yayansu biyu.

Isra’ila dai ta kai daruruwan hare hare a Siriya, tun bayan da kasar ta tsunduma cikin yaki a shekarar 2011.

Ko a tsakiyar watan Janairun nan, Isra’ila ta kai wasu jerin hare hare a yankin Deir Ezzor na Siriya wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 57, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama ta Siriya (OSDH), dake da cibiya a Biritaniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!