CRA : An Kafa Dokar Ta Baci, Saboda Barazanar ‘Yan Tawaye

2021-01-22 16:06:41
CRA : An Kafa Dokar Ta Baci, Saboda Barazanar ‘Yan Tawaye

Gwamnatin Afrika ta tsakiya ta sanar da kafa dokar ta baci ta twawon kwanaki 15, a duk fadin kasar, a wani mataki data ce na tunkarar barazanar gungun kungiyoyin ‘yan tawaye, da shugaban kasar Faustin Archange Touadéra, ya alakanta ‘yan ta’adda.

‘Yan tawayen na yunkurin shiga Bangui babban birnin kasar, wanda hakan babbar barazana ne cewar MDD, tare da bukatar kara yawan dakarun MDD, dake kasar.

Manyan kungiyoyin ‘yan tawayen da suka hade a wani kawance mai suna CPC, na rike da ikon kashi biyu cikin uku na kasar dake fama da yakin basasa na kusan shekaru 8.

‘Yan tawayen dai sun saka kafar wando guda da gwamnatin kasar ne gabanin zaben shugaban kasar na watan Disamba da ya gabata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!