Korona Ta Kama Mai Dakin Sheikh Zakzaky A Gidan Yarin Kaduna

Rahotanni daga Nijeriya suna nuni da cewa uwargidan shugaban harkar Musulunci a Nijeriyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, malama Zeenat El-Zakzaky ta kamu da cutar nan ta COVID-19 da aka fi sani da Coronavirus a gidan yarin Kaduna inda ake tsare da ita da maigidan nata.
Hakan
dai yana cikin wata wasika ne da dan Sheikh Zakzakin, wato Muhammad Ibrahim
Zakzaky ya fitar inda ya ke bayanin halin da mahaifiyar tasa take ciki.
Muhammad
ya ce lamarin ya faro ne bayan da mahaifiyar tasa ta fara korafin cewa tana
fama da zazzabi, gajiya da kuma rashin jin kamshin abubuwa, inda likitoci suka
yanke shawarar gudanar da bincike daban-daban don gano mece ce matsalar. Daga
cikin binciken da aka gudanar kanta har da gwajin cutar ta COVID-19 inda daga
karshe dai gwajin ya fito cewa Malama Zeenat din ta kamu da cutar.
Muhammadu
Zakzaky yayi korafi kan irin halin da mahaifan nasa suke ciki da kuma irin
rikon sakainar kashin da mahukunta masu kula da gidan yarin suke yi dangane da
halin da iyayen nasa suke ciki wanda ya bayyana hakan a matsayin wani kokari na
karasa su saboda irin halin rashin lafiya da daman suke fama da shi.
Babban
dan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya nuna tsananin damuwarsa dangane da irin yadda
aka ki kwantar da mahaifiyar tasa a asibiti duk kuwa da irin munin cutar ta
COVID-19 da kuma bukatar da ake da ita na kula da masu irin wannan cutar.
Idan dai ana iya tunawa tun a shekarar 2015 ne dai mahukunta a Nijeriyan suke tsare da Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakin nasa bayan rikicin Zariya.