Ronaldo Ya Zama Wanda Ya Fi Cin Kwallaye A Tarihin Wasan Kwallon Kafa

Shahararren ɗan
wasan kwallon ƙafan nan na ƙasar Portugal wanda a halin yanzu kuma yake bugawa
ƙungiyar kwallon kafa ta Juventus ta ƙasar Itali, Cristiano Ronaldo ya zama dan
wasan da ya fi cin kwallaye a tarihin duniyar kwallon kafa, bayan ya jefa
kwallo guda a wasan karshe na gasar cin kofin Italiya da Juventus ta doke
Napoli da 2-0 da aka buga a jiya Laraba.
A halin yanzu adadin kwallayen da Ronaldon ɗan shekaru
35 a duniya, ya ci a wasannin da ya buga
wa ƙungiyar ƙwallon ƙasa na ƙasarsa da
kuma ƙungiyoyinƙwallon ƙafa daban-daban da ya buga wa wasa sun kai kwallaye 760
wanda hakan ya sanya shi a matsayi na farko bayan ya doke wanda da man yake
rike da kambin wato Josef Bican ɗan
ƙasar Czech wanda ya zura ƙwallaye 759 tsawon wasannin da yayi.
Bayanai dai sun bayyana cewar Ronaldo
ya ci waɗannan kwallayen ne cikin wasanni 1,040 da ya buga a hukumance, da suka
hada da kwallaye 118 a Manchester United, 450 da ya ciwa Real Madrid, 85 da ya ci
wa Juventus, da 5 da ya ci wa Sporting Lisbon ƙungiyar da ya soma bugawa wa
wasa, sai kuma kwallaye 102 da ya ciwa ƙungiyar kwallon ƙafa ta ƙasarsa
Portugal.
A halin yanzu dai baya ga Ronaldon Josef Bican ɗan ƙasar Czech wanda ya zura ƙwallaye 759 shi ne na biyu, sai kuma tsohon ɗan wasan Brazil ɗin nan Pele wanda ya zura ƙwallaye 757, sai kuma Lionel Messi ɗan ƙasar Argentina kuma mai buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona mai ƙwallaye 742.