Biden, Ya Soke Dokar Hana Wasu 'Yan Kasashen Musulmi Shiga Amurka

2021-01-21 10:31:37
Biden, Ya Soke Dokar Hana Wasu 'Yan Kasashen Musulmi Shiga Amurka

Sabon shugaban Amurka, Joe Biden, ya sanya hannu kan wasu sabbin dokoki sa’o’I kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 46 a jiya Laraba.

Wasu daga cikin kudurorin da M. Biden ya sanya wa hannu, sun yi hannun-riga da manufofin tsohon shugaban kasar Donald Trump.

Daga cikin dokokin akwai shirin sanya kafar wando guda da annobar korona, da dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, da fige da fice da dakatar da gina Katanga tsakanin iyakar kasar da Mexico.

Sabon shugaban Amurkar ya soke dokokin dake hana ‘yan wasu kasashen musulmai da wasu na Afirka shiga Amurka.

M. Biden ya kuma sauya tsauraran matakan da aka dauka tsawon shekaru hudu, kan zama dan kasa a Amurka.

A jiya ne dai aka rantsar da Biden, a matsayin sabon shugaban kasar ta Amurka.

Baya ga Biden kuma an rantsar da Kamala Haris, a matsayin mataimakiyarsa, wacce ita mace ta farko kana kuma bakar fata data fara rike wannan mukami a tarihin AMurka.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!