Yemen : An Kyamaci Matakin Trump Na Sanya Ansarullah A Jerin ‘Yan Ta’adda

2021-01-21 10:22:37
Yemen : An Kyamaci Matakin Trump Na Sanya Ansarullah A Jerin ‘Yan Ta’adda

A Yemen, daruruwan mutane suka gudanar da zanga zanga a Sanaa, babban birnin kasar domin yin tir da matakin gwamnatin Amurka mai barin gado, na sanya kungiyar Ansarullah, da aka fi sani da ‘yan Houtsis, a cikin jerin ‘yan ta’adda na duniya.

Zanga zangar dai na zuwa ne kwana guda bayan da matakin sanya kungiyar cikin jerin ‘yan ta’adda ya soma aiki, a daidai kuma lokacin sabon shugaban Amurkar Joe Biden, ya yi rantsuwar kama aiki.

A halin da ake ciki dai sabuwar gwamnatin Amurka, ta ce zata duba wannan batun cikin gaggawa, saboda fargabar tabarbarewar al’amuran jin kai a kasar ta Yemen da yaki ya daidaita.

Kasar Yemen, ta fada cikin yaki ne tun bayan da Saudiyya da kawayanta suka farma wa Yemen da yaki a cikin shekarar 2015.

Lamarin dai ya jefa kasar Yemen, cikin hali mafi muni a duniya, inji MDD, bayan haddasa hasarar rayukan dubban mutane da tilastawa milyoyin jama’ar kasar kaura.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!