Africa CDC Ta Fara Shirin Karbo Rigakafin COVID-19 Ga Kasashen Nahiyar

2021-01-21 10:19:05
Africa CDC Ta Fara Shirin Karbo Rigakafin COVID-19 Ga Kasashen Nahiyar

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC, ta sanar da shirin fara yin odar alluran rigakafin cutar COVID-19 ga dukkan mambobin kasashen kungiyar tarayyar Afrika AU.

Wannan yunkuri ne na sashen rarraba magunguna na Afrika wato AMSP, a madadin hukumar ta Africa CDC.

Matakin na zuwa ne mako guda bayan sanarwar da shugaban kasar Afrika ta kudu, kana shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU, Cyril Ramaphosa, ya fitar cewa, AU ta samu kashin farko na alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 270 karkashin shirin tawagar samar da rigakafin COVID-19 na Afrika wato AVATT.

Sanarwar da Afrika CDC ta fitar ta ce, sashen raba alluran na AMSP, a madadin Africa CDC, zai fara shirin odar rigakafin ga dukkan mambobin kasashen AU.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!