Iran:Atisayen 'Iktidar 99" Don Jefa Tsoro Ne A Cikin Zukatan Makiya Kasar

2021-01-20 22:55:05
Iran:Atisayen 'Iktidar 99" Don Jefa Tsoro Ne A Cikin Zukatan Makiya Kasar

Kakakin atisayen sojojin kasa na kasar Iran wanda aka sanyawa suna “Iqtidar 99” ya ce sakon wannan atisayen shi ne zaman lafiya ga kawayen Iran sannan tsoro da nadama ga makiyanta.

Majiyar muruyar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran a nakalto Burgediya Janar Amir Kiomars Sharafi yana fadar haka a jiya Talata.

Sharafi ya kara da cewa an yi amfani da makamai daban-daban a cikin atisayin, wadanda suka hada da jiragen daukan sojoji zuwa fagen fama, da makamai masu linzami daban-danban.

Har’ila yau Sharafi ya ce an yi amfani da makamai wadanda ake amfani da su kan tudu daban-daban.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!