Zarif:Ba Wani Jami’in Gwamnatin Iran Da Ya Tattauna Da Gwamnatin Amurka Sabuwa

2021-01-20 22:49:41
Zarif:Ba Wani Jami’in Gwamnatin Iran Da Ya Tattauna Da Gwamnatin Amurka Sabuwa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya musanta labarin da ke cewa jakadan kasar Iran a MDD ya tattauna da jami’an sabowar gwamnatin Amurka wacce ta kama aiki a yau Laraba.

Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta nakalto Zarif yana fadar haka bayan taron majalisar ministocin kasar a yau Laraba a nan birnin Tehran.

Kafin haka dai jaridar ‘Le Figaro’ ta kasar Faransa ta baga labarin cewa jakadan kasar Iran a MDD Majid Takhravanchi ya tattauna da wasu jami’an gwamnatin kasar Amurka sabuwa kan wasu al-amura wadanda suka hada da yarjejeniyar Nucliyar kasar wato JCPOA.

Zarif ya kara da cewa makonni uku da suka gabata, jakadan kasar Iran a MDD Majih Takhravanci yana nan kasar Iran, kuma bai tattauna da wata jiridar kasar wajen dangane da wannan batun ba.

Daga karshe ministan ya kammala da cewa Iran bata bukatar tattaunawa da gwamnatin Amurka dangane da yarjejeniyar nukliyar kasar. Amurka ta fice daga yarjejeniyar, ta sake dawowa cikinta, sannan ta ciki dukkan alkawulan da ta dauka a cikinta. Ba tare da sanya wani sharadi ba. Daga cikin alkawulan har da dauke wa kasar takunkuman zalunci da ta dora mata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!