Iraki:An Kama Shuwagabannin Kungiyar Daesh Guda Uku A Kirkuk Da Diyala

2021-01-20 22:41:43
Iraki:An Kama Shuwagabannin Kungiyar Daesh Guda Uku A Kirkuk Da Diyala

Majiyar jami’an tsaron kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an kama wasu fitattun shuwagabannin kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh guda 3 a lardunan Kirkuk da kuma Diyala.

Kamfanin dillancin labaran ‘Shafaq-News’ na kasar ta Iraki ya bayyana cewa jami’an tsaron kasar karkashin ma’aikatar cikin gida sun kama wasu manya manyan shuwagabannin kungiyar Daesh masu suna, Tarik, Sa’ad da kuma Hesam a lardunan Kirkuku da kuma Diyala.

Daya daga cikinsu, jami’in watsa labarai na kungiyar ta Deash ne a lardin Kirkuk, a yayinda sauran kuma sun jagorantan wasu hukumomi a gwamnatin Daesh a wadannan larduna.

Labarin ya kara da cewa wasu daga cikin mutanen uku sun tabbatar da cewa, suna da hannu cikin ayyukan ta’addancin da aka kaiwa jami’an tsaron kasar a shekara 2014.

Duk da cewa an kawo karshen kungiyar ta Daesh a kasar Iraki, amma har yanzun wasu daddaikun ‘ya’yan kungiyar su kan kai hare-haren sari ka noke a cikin kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!