​Ana Shirin Rantsar Da Biden A Matsayin Shugaban Amurka Na 46

2021-01-20 14:51:43
​Ana Shirin Rantsar Da Biden A Matsayin Shugaban Amurka Na 46

A Amurka, yau Laraba ne ake rantsar da zababen shugaban kasar Joe Biden, da kuma mataimakiyarsa Kamala Harris.

Za’a dai watsa bikin ne da aka takaita jama’a ta gidan talabijin.

Dan shekaru 78, Joe Biden, zai kasance shugaban Amurka na 46, bayan kada Donald Trump, a zaben shugabancin kasar na watan Nuwamban bara.

Ita kuwa Kamala Harris, zata kasance mace ta farko kuma bakar fata da zata rike mukammin mataimakin shugaban kasa a Amurka.

An dai tsaurara matakan tsaro na fitar hankali, a birnin na Washington, inda aka jibge dakaru kimanin dubu 25 domin kaucewa duk wata tarzoma, sakamakon abunda ya faru kwanan baya, inda magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump suka farmawa majalisar dokokin kasar.

Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kasar ta Amurka, sun hada da yaki da annobar korona dake ci gaba da kisa, da hada kan al’ummar kasar, da kuma maido da martabar Amurka da ta zube a idon duniya a lokacin mulkin Trump.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!