Korona ta kashe karin mutum 15 a Najeriya
2021-01-20 14:46:24

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 1,301 da suka kamu da annobar korona a kasar ranar Talata.
A cewar kuma
hukumar ta NCDC, akwai mutum 15 da cutar ta yi ajalisnu a cikin sa'o’i 24 da suka gabata.
Bisa sabbin
alkaluman hukumar, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu
da cutar sai kuma Abuja, babban birni.
Yanzu dai kididdigar masu cutar a Najeriya ita ce 113,305 sannan mutum 91,200 sun warke inda kuma mutum 1,464 suka rasu
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!