​Najeriya: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Da Ta Auku Kasuwar Babban Birnin

2021-01-20 10:18:37
​Najeriya: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Da Ta Auku Kasuwar Babban Birnin

Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa kwamitin bincike dangane da gobarar da ta auku a garin Sokoto a jiya, wadda ta jawo mummunan asara ta dukiyoyi.

Bayan faruwar lamarin a jiya, gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya halarci wurin domin ganewa idonsa hakikanin abin da ya faru, inda ya nuna kaduwarsa matuka.

Gwamnan ya ce; wannan gobara hakika babban abin bakin ciki ce, ya ce suna iyakar kokari domin ganin an takaita yawan hasara, kamar yadda kuma jami’an tsaro suna nan a wurin da abin ya faru, domin tabbatar da cewa ba a sace kayan jama’a ba, a kan haka ya ce jama’a su kara hakuri da wannan ibtila’i da ya auku.

Da dama daga cikin wadanda lamarin ya shafa sun bayyana cewa sun asarori masu tarin yawa, inda shaguna da dama suka kone kurmus da dukkanin kayayyakin da ke cikinsu.

Gwamnan Sokoto ya bayyana cewa tuni ya kafa kwamiti domin binciko hakikanin musabbabin wannan gobara, da kuma matakan da ya kamata a dauka domin kaucewa faruwar haka a nan gaba, da kuma kiyasta irin asarori da aka yi domin sanin irin tallafin da gwamnati za ta bayar ga wadanda lamarin ya shafa.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!