​Avril Haynes: Zan Mika Rahoto Kan Masu Hannu A Kisan Jamal Khashoggi

2021-01-20 09:30:14
​Avril Haynes: Zan Mika Rahoto Kan Masu Hannu A Kisan Jamal Khashoggi

Jami’ar da za ta rike mukamin babbar darakta ta hukumomin leken asirin kasar Amurka a gwamnatin Joe Biden Avril Haynes ta bayyana cewa, za ta gabatar da cikakken bayani kan masu hannu a kisan Jamal Khashoggi.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Avril Haynes ta bayyana cewa, za ta gabatar da cikakken rahoto kan dukkanin masu hannu a kisan da aka yi wa dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, a cikin cikin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya a birnin Istanbul na kasar Turkiya a 2018.

Avril Haynes ta bayyana hakan ne a jiya gaban majalisar dattijan Amurka a lokacin da take amsa tambayoyi kan lamurra da suka shafi aikin da za a damka mata, inda sanata Ron Wyden ya tambaye ta kan cewa, shin tana da shirin bayar da bayanan sirri kan kisan Khashoggi, inda ta amsa da cewa tabbas za ta mika cikakken rahoto kan hakan.

Ana sa ran dai rahoton na Avril Haynes wanda za ta mika wa majalisar dattijan Amurka, zai kunshi wadanda suke da hannu a cikin kisan Jamal Khashoggi, da kuma wanda ya bayar da umarnin yin hakan, da kuma yadda aka aiwatar da kisan.

Batun kisan gilar da aka yi Jamal Khashoggi dai yana daya daga cikin batutuwan da aka yi ta kai ruwa rana a kansu tsakanin Trumkp da ‘yan majalisar dattijai, inda Trump din yaki amincewa da a mika wa majalisa bayanan sirri kan batun, wanda ake zargin yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman da hannu kai tsaye wajen bayar da umarnin yin kisan.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!