Sojojin Ƙasa Na Iran Sun Fara Gagarumin Atisayen Soji A Kudu Masu Gabashin Ƙasar

2021-01-19 20:26:21
Sojojin Ƙasa Na Iran Sun Fara Gagarumin Atisayen Soji A Kudu Masu Gabashin Ƙasar

Dakarun sojojin ƙasa na ƙasar Iran sun ƙaddamar da wani sabon atisayen don tabbatar da irin shirin ko ta kwana da suke da shi na tabbatar da tsaro ƙasar da kuma kare ta daga dukkanin barazanar maƙiya.

A yau Talata ce dai aka fara wannan atisayen wanda aka ba shi sunan Eqtedar (ƙarfi da tsayin daka) 99, a yankin bakin ruwa na Makran da ke kudu maso gabashin ƙasar ta Iran bisa jagorancin babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar Manjo Janar Abdolkarim Mousavi da kuma babban hafsan hafsoshin sojojin ƙasa na ƙasar ta Iran Birgediya Janar Kioumars Heydari.

Dakarun da suke gudanar da atisayen sun haɗa da dakarun sama, dakaru na musamman da kuma dakarun ko ta kwana na sojojin na Iran bisa taimako da kuma ɗaukin sojojin sama na ƙasar Iran.

A yayin atisayen za a gwada wasu dabarun yaƙi daban-daban don gwada irin ƙwarewa da kuma ƙarfin da dakarun sojin na Iran suke da shi, kamar yadda kuma za a yi amfani da ɗaruruwan sojojin ‘yan sama jannati da ake sako su daga sama daga cikin jiragen ɗaukan kaya na sojojin da sauke su a wasu wajajen da aka tsara don su kai farmaƙi ga sojojin abokan gaba.

Yayin da yake magana kan atisayen, babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar Manjo Janar Abdolkarim Mousavi ya bayyana cewar jerin atisayen da dakarun Iran suka gudanar cikin kwanakin da suka gabata suna a matsayin wani jan kunne ne ga maƙiyan al’ummar Iran da cewa duk wani ƙoƙarin wuce gona da iri na maƙiya zai fuskanci gagarumin mayar da martani daga wajen dakarun na Iran.

Shi ma a nasa ɓangaren, babban hafsan hafsoshin sojojin ƙasa na ƙasar ta Iran Birgediya Janar Kioumars Heydari, ya bayyana cewar manufar atisayen ita ce tabbatar da irin ƙarfi da kum shirin ko ta kwana da dakarun na Iran suke da shi, yana mai cewa saƙon sojojin Iran ga maƙiya shi ne cewa suna ci gaba da sanya kan duk wani motsinsu sannan kuma yatsun sojojin na Iran suna kan kunaman bindigoginsu, kuma za su mayar da martani daga lokacin da buƙatar hakan ta taso.

A makon da ya wuce ma sojojin ruwa na sojojin na Iran sun gudanar da wani gagarumin atisayen soji a kogin Oman inda a nan ma suka gwada wasu daga cikin ƙarfi da dabarun yaƙi da suke da su.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!