Shugaban Tunusiya Ya Buƙaci ‘Yan Kasar Da Su Kawo Ƙarshen Zanga-Zangar Da Suke Yi

2021-01-19 20:04:19
Shugaban Tunusiya Ya Buƙaci ‘Yan Kasar Da Su Kawo Ƙarshen Zanga-Zangar Da  Suke Yi

Shugaban ƙasar Tunusiya Kais Saied ya buƙaci al’ummar ƙasar da su kawo ƙarshen zanga-zangar da suke yi yana mai kiransu da cewa su yi taka tsantsan kada su bari wasu su yi amfani da matsalolin da suke ciki don cimma manufofinsu na ƙashin kai.

Shugaban na Tunusiya ya bayyana hakan ne a yau Talata a wata ziyara da ya kai garin Ariana da ke kusa da birnin Tunis, babban birnin ƙasar, inda cikin jawabin da yayi ya shaida wa al’ummar ƙasar cewa lalle yana sane da irin talauci da matsin lambar da al’umma suke ciki, kamar yadda kuma yana sane da waɗanda suke son amfani da wannan yanayin don cimma manufofinsu. Don haka sai ya buƙaci al’ummar da su yi taka tsantsan kada su bari wasu su yi amfani da su wajen cimma manufofinsu.

Har ila yau shugaba Saied ya kirayin ‘yan ƙasar da su guji kai hari kan kadarori na jama’a da kuma na gwamnati wanda ya ce hakan ya saɓa wa halaye da ɗabi’un mutanen ƙasar.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ce dai mutanen ƙasar Tunusiya a wasu garuruwa na ƙasar da suka haɗa da Kasserine, Tunis da sauran manyan birane suke ta gudanar da zanga-zangogi don nuna rashin amincewarsu da yawaitar rashin aikin yi da kuma matsaloli na tattalin arziki da yayi musu katutu a ƙasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnati ta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake tarzomar da nufin kwantar da ita, inda ya zuwa yanzu an kama wani adadi mai yawa na masu tarzomar.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ce dai al’ummar ƙasar Tunusiyan suka gudanar da bukukuwan shekaru 10 da fatattakan tsohon shugaban mulkin kama karya na ƙasar, Zainul Abidin Bin Ali daga ƙasar bayan zanga-zangar da al’ummar ƙasar suka dinga yi don nuna ƙyamar gwamnatinsa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!