Qatar: Lokaci Ya Yi Da Za A Bude Tattaunawa Tsakanin Iran Da Kasashen Yankin Tekun Fasha

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana
cewa, lokaci ya yi da za a bude tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da kasashen yankin tekun fasha.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, ministan
harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al-Thani ya bayyana cewa, kasar
Qasar na da imanin cewa, ya zama wajibi a gudanar da tattaunawa tsakanin Iran
da kasashen yankin tekun fasha, domin samun fahimtar juna.
Ya ce, gudanar da irin wannan
tattaunawar zai bayar da damar cimma abubuwa da dama da za su amfanar da kasashen
yankin baki daya, musamman ma ganin cewa akwai canje-canje da dama ta fuskacin
siyasa da za su iya faruwa a yankin, sakamakon samun canjin gwamnati a kasar
Amurka.
Ministan harkokin wajen kasar ta
Qatar ya ce, kasarsa za ta bayar da dukkanin gudunmawar da ta kamata domin
ganin cewa an cimma wannan buri, kuma za ta ci gaba da tuntubar dukkanin bangarorin
yankin, inda yanzu haka wasu daga cikin kasashen yankin sun bayyana aniyarsu ta
shiga tattaunawa kai tsaye tare da kasar ta Iran.
Tun kafin wannan lokacin dai
gwamnatin kasar ta Iran ta sha nanata cewa a shirye take ta shiga tattaunawa
tare da dukkanin kasashen yankin tekun fasha domin samun maslaha da kuma
warware batutuwa da dama da suke kawo tarnaki wajen ci gaban alaka tsakaninsu,
amma bisa matsin lambar kasashen turai, kasashen yankin ba su bayar da hadin
kai ga kiran na kasar Iran ba.
015