​Lebanon Ta Mayar Wa Isra’ila Da Martani Kan Kiran Hizbullah Da Kungiyar Ta’addanci

2021-01-19 13:38:06
​Lebanon Ta Mayar Wa Isra’ila Da Martani Kan Kiran  Hizbullah Da Kungiyar Ta’addanci

Wakilin kasar Lebanon a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya mayar wa wakiliyar Isra’ila a kwamitin da kakkausan martani, bayan da ta kira kungiyar Hizbullah da sunan kungiyar ta’addanci.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya, Wakilin kasar Lebanon a kwamitin Salim Badurah, ya caccaki wakiliyar Isra’ila a kwamitin, sakamakon sukar kungiyar Hizbullah da ta yi.

Salim ya ce kungiyar Hizbullah bangare ne mai matukar muhimmanci a kasar Lebanon, da ke taka muhimmiyar rawa a dukkanin bangarori na siyasa, da zamantakewar al’ummar kasar, kamar yadda kuma kungiyar tana a matsayin babban jigo na gwagwarmaya da mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunan kasar Lebanon.

Ya ce Isra’ila ita ce tarihinta yake ciki da munanan ayyuka na kisan gilla da cin zarafin ‘yan adam, da mamaye yankunan Falastinawa da yi musu kisan kiyashi, wanda hakan lamari ne a bayyane ga dukkanin al’ummomin duniya.

Wakiliyar Isra’ila a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta bayyana kungiyar Hizbullaha matsayin kungiyar ta’addanci, wadda take yin barazana ga zaman lafiyan yahudawan Isra’ila da kawayensu a yankin gabas ta tsakiya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!