Sojin Aljeriya Sun Yi Wani Gagarimin Atisaye A Iyaka Da Yammacin Sahara

2021-01-19 09:30:33
Sojin Aljeriya Sun Yi Wani Gagarimin Atisaye A Iyaka Da Yammacin Sahara

Watanni kadan, bayan da kasar Morocco ta sanar da dawo da alaka da Isra’ila, sojojin Aljeriya, sun fara wani gagarimin atisayen soji a iyaka da yammacin sahara.

Atisayen wanda ya gudana a ranakun Lahadi da Litini, a yankin Tindouf, dake kudancin kasar, ya kunshi gwaje gwaje motoci masu sulke, da jiragai masu saukar ungulu, da na yaki da kuma harbe harben makamai masu linzami.

Kasar Aljeriya dai na nuna damuwa akan yiyuwar aukuwar rikici a tsakanin iyakokinta, tun dai bayan da aka shiga halin rashin tabbas a yammacin sahara, wanda bai rasa nasaba da barazanar da Aljeriyar ke cewa tana fuskanta daga wasu kasashen waje musamman Isra’ila, bayan da Amurka ta amince da ikon Morocco a yankin ‘yan Saharawi, bayan data amince da sake kulla alaka da Isra’ila.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!