Tunusia : An cafke Masu Boren Dare Sama Da 600

2021-01-19 09:28:06
Tunusia : An cafke Masu Boren Dare Sama Da 600

Hukumomi a Tunusia, sun ce sama da mutane 600 ne aka cafke yayin boren da aka kwashe kusan kwanaki hudu anayi a wasu sassan kasar.

Rahotanni daga kasar sun ce an sha arangama tsakanin jami’an tsaro da matasa masu boren duk da dokar hana fitar dare da aka kafa.

Galibin wadanda aka cafken matasa ne ‘yan tsakanin shekara 15 zuwa 25, wadanda ke kone konen tayoyi.

Lamarin ya yi kamari a wasu sassan kasar inda har ta kai ga jibge sojoji domin tabbatar da doka da oda.

Boren dai ya barke ne a wasu sassan kasar dake ci gaba da fama da matsin tattalin arziki, shekaru 10 bayan kifar da mulkin shugaba Ben Ali.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!