Tashin Bam Ya Yi Ajalin Sojin Nijar 4, A Tafkin Chadi

2021-01-19 09:24:29
Tashin Bam Ya Yi Ajalin Sojin Nijar 4, A Tafkin Chadi

Hukumomin tsaro a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da mutuwar sojojin kasar hudu, sanadin taka wani abun fashewa a Chetima Wongo dake a kusa da tafkin Chadi.

Lamarin dai ya faru ne a cikin daren Lahadi wayewar safiyar Litini, yayin da sojojin suka murkushe wani wunkurin kungiyar boko haram na kai hari kan sansanin sojin Chetima Wongo, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, kamar yadda gidan radiyon faransa na rfi, sashen faransanci ya nakalto.

Baya ga sojojin hudu da suka rasa rayukansu da akwai da dama da suka jikkata wanda yanzu haka suke karbar magani.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!