Zarif: Iran Ba Zata Yi Taraddudin Murkushe Makiya Kasar Ba, Idan Sun Farwa Kasar Da Yaki

2021-01-18 19:57:54
Zarif: Iran Ba Zata Yi Taraddudin Murkushe Makiya Kasar Ba, Idan Sun Farwa Kasar Da Yaki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammada Javad Zarif ya bayyana cewa kai kawon da jiragen yakin Amurka Samfurin B-52 suka yi ta yi a kan tekun Farisa a cikin yan kwanakin da suka gabata, ba zai hana Iran murkushe sojojin Amurka idan sun kuskura suka farwa kasar da yaki ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif yana cewa, sojojin kasar Iran da dakarun kare juyin juya halin musulunci, wato (IRGC) na kasar, sun nuna karfin sojojin kasar a cikin kwana 10 da suka gabata, don tabbatarwa makiya cewa kasar Iran ba kanwan lasa bace.

Har’ila yau babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Janar Mohammad Bakiri ya bayyana cewa shawagin da jiragen yakin Amurka Samfurin B-52 suka yi ta yi a yankin gabas ta tsakiya a cikin yan kwanakin da suka gabata, wata takala ce daga gwamnatin shugaban Trump wacce wa’adinta yake karewa.

Janar Bakiri ya kara da cewa sojojin kasar Iran zasu ci gaba da atisayin nuna korewa da kuma shirin kare kasar a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.(19)

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!