Sudan:Masu Zanga-Zanga Sun Kona Tutar Isra’ila Saboda Kin Jininta.

2021-01-18 19:41:52
Sudan:Masu Zanga-Zanga Sun Kona Tutar Isra’ila Saboda Kin Jininta.

Masu zanga-zanga a birnin Khartum babban birnin kasar Sudan sun kona tutar haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) a gaban majalisar dojojin kasar a jiya Lahadi, tare da nuna rashin amincewarsu da samar da huldar jakadanci da haramtacciyar kasar.


Tashar talabijin ta Almayadeen, wacce take watsa shirye-shiryenta da harshen larabci daga kasar Lebanon ta bayyana cewa masu zanga-zangar wadanda suka bayyana kansu a matsayin wadanda suke wakiltar mutanen kasar Sudan don nuna turjiya dangane da hulda da HKI, sun je gaban ofishin firai ministan kasar Andallah Hamduk inda suke dauke da rubuce-rubuce masu cewa “Ba ma son hulda da Isra’ila” ba mason mika kai ga Amurka da sauransu.

A ranar 23 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce, Amurka ta tursasawa gwamnatin kasar Sudan samar da huldar jikadanci da HKI kafin ta cire sunan kasar daga jerin kasashe masu goyon bayan ayyukan ta’addanci a duniya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!