MDD Ta Bayyana Damuwarta Da Yadda Kamfanonin Samar Da Alluran Riga Kafin Korona Suke Rarrabata

2021-01-18 19:33:24
MDD Ta Bayyana Damuwarta Da Yadda Kamfanonin Samar Da Alluran Riga Kafin Korona Suke Rarrabata

Babban sakatarin MDD Antonio Guterres ya bayyana rashin amincewarsa da yadda kamfanonin samar da alluran riga kafin cutar korona a duniya suke rarraba alluran.

Majiyar muryar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Antonio Guterres yana fadar haka a jiya Lahdi, ya kuma kara da cewa, kamfanonin sun himmatu da manya-manyan kasashen duniya masu arziki, a yayinda suka kuma manta da kananan kasashen a duniya.

Babban sakataren ya bukaci wadannan kamfani su yi adalci a rabon alluran riga kafin tsakanin kasashen duniya ba tare da nuna wariya ba.

Ya kara da cewa a dai-dai lokacinda wasu kasashen da basa da karfi basu sami alluran ba, wasu kasashen masu arziki suna sayan fiya da bukatarsu.

MDD da kuma hukumar lafiya ta duniya, (WHO) duk sun nana damuwarsu da yadda ake rabon alluran riga kafin cutar ta korona a duniya, sun kuma kara da cewa rashin rara shi cikin adalci ba zai amfani duniya ba, don wanzuwar cutar a wata kasa a duniya zai sa ta sake yaduwa. (19)

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!