Ghana Da Iran Sun Tattauna Kan Hanyoyin Bunkasa Harkokin Noma

2021-01-18 14:59:37
Ghana Da Iran Sun Tattauna Kan Hanyoyin Bunkasa Harkokin Noma

Kasashen Iran da Ghana, na tattaunawa a wani mataki na bunkasa harkokin noma a tsakaninsu.

Wannan bayanin ya fito ne bayan wani taro da jami’an kasashen biyu sukayi a makon da ya gabata a birnin Accra na kasar Ghana.

Karamin ministan harkokin noma na Iran, Shahrokh Shajari, shi ne ya jagoranci tawagar Iran a taron tare da jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar Ghana.

Yayin taron bangarorin biyu, sun jaddada mahimancin karfafa alakar dake tsakanin kasashen a bangaren noma, ciki harda musayar fasaha a bangaren da kasashen Afrika.

An kiyasta harkokin kasuwanci tsakanin Iran da Afrika, ya kai tan dubu 960 a tsakanin watan Maris zuwa Oktoba na bara, wanda ya kai na dala kimanin miliyan 180.

Ghana kuma ita ce kasar Afrika, ta farko dake yo odan haja daga Iran wanda yake kaiwa har na dala miliyan 52,8.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!