​Sudan: Akalla Mutane 83 Suka Rasa Rayukansu A Tarzomar Da Ta Barke A Darfur

2021-01-18 09:37:26
​Sudan: Akalla Mutane 83 Suka Rasa Rayukansu A Tarzomar Da Ta Barke A Darfur

Majiyoyin tsaro a Sudan sun ce akalla mutane 83 ne suka rasa rayukansu a tarzomar da ta barke a yankin Darfur da ke yammacin kasar.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, hukumomin tsaro na kasar Sudan sun tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya kaule a yankin Darfur da ke yammacin kasar, ya kai mutane 83, yayin da wasu kimanin 160 kuma suka samu munanan raunuka.

An yi arangama mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da kuma wasu masu tayar da tarzoma, sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a garin Aljanina da ke cikin yankin Darfur na kasar Sudan.

Rikicin ya barke ne biyo bayan wata takaddama tsakanin wasu mutane biyu, wanda ya kai ga kisan kai, daga nan kuma lamarin ya rikide ya koma rikici tsakanin kabilu.

Yanzu haka dai jami’an tsaro suna ci gaba da yin sintiri a daukacin yankin, tare da kafa dokar ta baci a yankin baki daya.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!