Najeriya: Sojoji Sun Ce Sun Ragargaza Wata Kwamba Ta Motocin Boko Haram

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta
bayyana nasarar ragargaza motocin yaki bakwai na Boko Haram da aka yi ta hanyar
amfani da jiragen yaki.
Jaridar Premium Times ta bayar da
rahoton cewa, Kakakin Hedikwatar Tsaron ta Kasa, John Enenche ne ya bayyana
haka a cikin wata danarwa da ya fitar.
Ya ce an ragargaza jerin gwanon
kwamba din motocin yakin ne a lokacin da su ke kokarin karasawa garin Marte da
ke jihar Barno, domin su kai wa wasu Boko Haram agajin karin mahara.
Ya ce sojojin Operation Lafiya Dole
ne su ka kai farmaki kan Boko Haram din wadanda aka tabbatar cewa bangaren
’yan ta’addar ISWAP ne.
Cikin sanarwar da ya fitar ranar
Lahadi, Enenche ya ce an ragargaza motocin ISWAP din har mota bakwai bayan da
farko an lalata wasu bakwai.
Manjo Janar Enenche a ce kwanaki
biyu a jere, tsakanin ranr 15 da 16 Ga Janairu, sojojin Njaerfiya sun yi
gagarimar nasarar hana ISWAP Shiga garin Marte.
Sai dai baya ga bayanin rundunar sojin ta Najeriya, babu wasu kafofi masu zaman kansu da suka kawo wannan labarin daga bangarensu.
015