Bobi Wine Ya Kirayi Magoya Bayansa Da su Guji Tada Hankali, Zai Ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen A Kotu

2021-01-17 18:28:45
Bobi Wine Ya Kirayi Magoya Bayansa  Da su Guji Tada Hankali, Zai Ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen A  Kotu

Madugun ‘yan adawan ƙasar Ugandan Bobi Wine ya buƙaci magoya bayansa da su guji duk wani nau’i na tashin hankali yana mai cewa zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka sanar a kotu.

Bobi Wine ya bayyana hakan ne a yau ɗin nan Lahadi cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin jam’iyyarsa ta National Unity Platform (NUP) na Twitter inda ya shaida wa magoya bayansa cewa: Duk da cewa abin da ya farun wani lamari ne mai sosa rai, amma dai ina kiranku da ku guji duk wani nau’i na tashin hankali a daidai lokacin da muke shirin ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu.

Bobi Wine wanda asalin sunansa shi ne Robert Kyagulanyi ya ce ya ɗau wannan mataki ne bayan tattaunawa da jagororin jam’iyyar ta NUP.

A jiya ne dai hukumar zaɓe na ƙasar Ugandan ta sanar da cewa shugaban ƙasar Yoweri Museveni ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Alhamis ɗin da ta gabata bayan ya samu kashi 58.6 cikin ɗari na kuri’un da a ka kaɗa alhali shi kuma Bobi Wine ɗin ya samu kashi 34.8 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa ɗin.

Madugun ‘yan adawan dai ya yi zargin an tafka maguɗi yayin zaɓen kamar yadda kuma yayi zargin jami’an tsaro sun yi wa gidansa ƙawanya da kuma hana shi duk wata dama ta ganawa da magoya bayansa. Sai dai jami’an tsaron musamman sojojin ƙasar sun musanta wannan zargin suna masu cewa sun je gidan nasa ne don ba shi tsaro a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa.

Tun shekara ta 1986 ne dai shugaban Museveni, ɗan shekaru 76 a duniya, yake mulkin ƙasar Ugangan lamarin da ya sanya shi cikin shugabannnin Afirka da suka fi daɗewa bisa karagar mulki.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!