Biden Zai Soke Wasu Dokokin Trump Ciki Kuwa Har Da Dokar Hana Wasu Musulmin Shiga Amurka

2021-01-17 18:26:35
Biden Zai Soke Wasu Dokokin Trump Ciki Kuwa Har Da Dokar Hana Wasu Musulmin Shiga Amurka

Rahotanni daga Amurka sun bayyana cewar shugaban ƙasar mai jiran gado Joe Biden zai soke wasu dokokin da shugaban ƙasar mai barin gado Donald Trump ya kafa ciki kuwa har da dokar hana musulmin wasu ƙasashen musulmi zuwa Amurkan.

Wannan labarin yana cikin wata takarda ce da sabon shugaban ma’aikata na Fadar White da Joe Biden ɗin ya naɗa, Ron Klain ya raba wa manema labarai inda ya ce cikin kwanaki goman farko na sabuwar gwamnatin ta Biden za ta soke wasu daga cikin dokokin da Trump ɗin ya kafa a lokacin mulkinsa.

Baya ga dokar hana musulmin wasu ƙasashen musulmin shiga Amurka, har ila yau daga cikin dokoki da kuma siyasar Trump ɗin da Joe Biden ɗin zai yi watsi da su sun haɗa har da dokar ficewa daga yarjejeniyar dumamar yanayi inda Joe Biden ɗin zai sake dawo da Amurka cikin yarjejeniyar bugu da ƙari kan wasu dokoki na shige da fice da za su ba wa wasu mutane kimanin miliyan huɗu sakamakon takardar ‘yan ƙasa na Amurka.

Jin kaɗan bayan ɗarewarsa karagar mulki, a shekara ta 2017, Trump ya ba da umurnin hana wasu matafiya daga wasu ƙasashen musulmi bakwai zuwa Amurkan lamarin da ya janyo kace-nace sosai.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!