An Shiga Rana Ta Biyu Ta Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka Da Ake Bugawa A Kamaru

2021-01-17 18:18:03
An Shiga Rana Ta Biyu Ta Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka Da Ake Bugawa A Kamaru

A yau Lahadi ne aka shiga rana ta biyu ta gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka da aka buɗe shi a jiya Asabar a ƙasar Kamaru inda a jiyan Kamarun ta samu nasara a kan ƙasar Zimbabwe.

A wasan na yau dai ƙasashen da suke group na B ne za su fafata inda a wasan farko za a kara tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa na ƙasar Libiya da na Jamhuriyar Nijar, sai kuma wasa na biyu da za a kara tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Demokraɗiyyar Kongo da kuma ƙasar Kongo.

A wasan da aka buga a jiya Asabar a matsayin wasannin buɗe gasar, ƙasar Kamaru mai masauƙin baƙi ta samu nasarar a kan abokiyar karawarta ta ƙasar Zimbabwe da 1-0.

Wasa na biyu da aka buga a jiyan kuma an buga ne tsakanin ƙasashen Mali da Burkina Faso inda ƙasar Mali ɗin ta samu nasara kan Burkina Fason da 1-0.

A gobe litinin ma dai za a buga wasanni biyu ne. Wasan farko za a buga shi ne tsakanin ƙasashen Moroko da Togo sai kuma wasa na biyu tsakanin ƙasashen Rwanda da Uganda.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!