​Taron Zaman Makokin Ranar Shahadar Fatima Zahra (AS)

2021-01-17 11:14:44
​Taron Zaman Makokin Ranar Shahadar Fatima Zahra (AS)

A yau ne ake gudanar da zaman makokin ragayowar ranar shahadar Sayyid Fatima Zahra diyar manzon Allah (SAW) a kasar Iran da ma wasu daga cikin kasashen musulmi.

An gudanar da zaman makokin a daren jiya a Husainiyar Imam Khomeni tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

A rana irin ta yau 3 ga watyan Jumada Thani, shekaru 11 bayan hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina, Sayyida Fatima Zahra diyar manzon Allah ta yi shahada a birnin Madina, wato shekara daya bayan wafatin mahaifinta manzon Allah (SAW).

An haifi Sayyida Fatima Zahra shekaru 5 ne bayan aiko manzon Allah (SAW) a makka, inda mahaifiyarta Khadijatul Kubra (AS) matar manzon Allah ta kasance ita ce babban mai karfafa gwiwar ma’aiki tare da taimaka masa tun daga cikin gidansa dangane aikin isar da sakon ubangiji ga talikai.

Sayyida Fatima Zahra ta kasance tare da mahaifinta manzon Allah a dukkanin rayuwarta ta kuruciya, kuma ta samu tarbiya a hannunsa da kuma hannun mahaifiyarta Khadijatul Kubra.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!